Game da mu
Gidan Radiyon kasar Iran, wani kamfani ne na kafar watsa labaran Iran din, wanda ke da niyyar siffanta sahihin yanayin kasar Iran da kuma al’amuran duniya baki daya. Dimbin sassan wannan kamfani mai tarin yawa da ke da sautuka da sauran kafafan watsa labarai, suna ba da damar bayyana bangarori daban-daban na kasar Iran kamar dai na siyasa, al’amuran tattalin arziki da al’adu, waɗanda galibi ake yin watsi da su ko kuma rashin fahimtarsu ta hanyar manyan kafofin watsa labarai. Haka nan ya shafi lamurran duniya don ba da ra’ayoyi daban-daban, game da mahangar kasar Iran din. Radiyon kasar Iran yana ba wa waɗanda suka kosa da labaru na al’ada, kuma masu neman madadan wasu muryoyi ingantattu! Mai dauke da harsuna sama da 25, Radiyon na kasar Iran din ya tsawaita isar da sakonsa ta hanyar yanar-gizon da dandamalin kafofin watsa labaru daban-daban. Kafar tana aiki ne daga babban birnin kasar na Tehran. Wannan kamfanin yana samun tallafi ne daga sassan hukumomin gwamnati da kungiyoyin al’adu masu zaman kansu, don tabbatar da samar da kayayyaki da ayyuka masu inganci.